On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Wasu hare-haren 'yan bindiga sunyi ajalin mutane da dama a jihar Fulato

Hukumomi sun ce an tura ƙarin jami'an tsaro a yankin


Rahotanni na nuni da cewa an  kashe mutane 135 yayin wasu hare-hare da 'yan bindiga suka kai a wasu ƙauyuka na Jihar Fulato a ranar Lahadi.

Maharan wadanda sukayi amfanj da babura sun far wa a aƙalla ƙauyuka hudu a Ƙaramar Hukumar Kanam, inda suka dinga harbe mutane tare da ƙona gidaje masu ɗumbin yawa da kuma sace shanu.

Har yanzu Babu cikakken bayanai daga hukumomi a jihar game da hare-haren.

Sai dai wani basaraken gargajiya a yankin ya shaida wa BBC cewa tuni aka gano gawar mutum 54 a kauyen Kukawa da kuma gawar mutum 34 a kauyen Gyambau. 

Bayanai sun nuna cewa cikin wadanda aka kashe har da kananan yara da matasa.

Mutane da dama ne suka ɓace sakamakon harin yayin da lamarin ya raba daruruwan mutane daga muhallansu.

Mazauna yankin sun yi zargin cewa an kwasshe kusan kwana guda kafin jami'an tsarto su kai musu dauki.

Sun kara da cewa wadannan su ne hare-hare mafiya muni da aka taba kai wa a yankin.

Hukumomi sun ce an tura ƙarin jami'an tsaro a yankin.

Ya kara da cewa an kashe mutum talatin da daya a wasu kauyuka biyu.

Kana an kashe 'yan kato-da-gora akalla 16 a kauyen Shuwaka.